Amurka

Trump zai kammala yininsa na karshe a fadar White House

Donald Trump, Shugaban Amurka mai barin gado
Donald Trump, Shugaban Amurka mai barin gado MANDEL NGAN AFP

Yau Shugaban Amurka mai barin gado, Donald Trump ke kammala yininsa na karshe a fadar shugaban kasa kafin rantsar da zababben shugaban kasa Joe Biden gobe laraba, a daidai lokacin da ake saran Biden ya bar garin su na Delaware domin isa birnin Washington inda zai karbi rantsuwa.

Talla

Rahotanni sun ce kusan mako guda kenan ba’a ga Trump a bainar jama’a ba, yayın da kafar twitter ta dakatar da sakonnin da ya saba aike wa jama’a saboda zargin da aka masa na tinzira magoya bayansa su yi bore a Majalisar dokoki.

Masu sanya ido kan harkokin shugaban sun ce babu wata hira ta waya, ko ta kafar talabijin da aka shirya wa shugaban mai barin gado a tashar Fox News wadda ta shahara wajen goyan bayan Trump.

Ya zuwa yanzu dai shugaba Trump bai taya Joe Biden murnar nasarar da ya samu ba a bayyane, ko taya shi murna ko kuma gayyatarsa fadar shugaban kasa domin shan shayi kamar yadda aka saba.

Rahotanni sun ce yanzu haka shugaban na can yana nazarin yi wa wasu tarin mutanen da aka samu da laifi afuwa, ciki har da shi kan sa wanda bincike ya nuna cewar yaki biyan haraji kamar yadda doka ta tanada.

Bayanai sun ce Biden wanda zai isa Washington da uwargidan sa Jill zai yi jawabi kan cutar korona daga Cibiyar tunawa da tsohon shugaba Abraham Lincoln.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.