Amurka

Kamala Harris ta zama abin alfahari ga mata

Sanata Kamala Harris, mace ta farko da ta rike mukamin mataimakiyar shugaban kasar Amurka
Sanata Kamala Harris, mace ta farko da ta rike mukamin mataimakiyar shugaban kasar Amurka REUTERS/Elijah Nouvelage

A yayin da Amurkawa ke shaida kafuwar sabuwar gwamnatin Jam’iyyar Democrats a wannan Laraba, a yau din ne kuma Kamala Harris ta kafa tarihin zama mace ta farko da ta rike mukamin mataimakiyar shugaban kasar Amurka, a tarihin kasar.

Talla

Kamala Harris da mata a ciki da wajen Amurka ke kallo a matsayin abar koyi, ta taka muhimmiyar rawa wajen kawo karshen gwamnatin shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump.

Daga cikin hanyoyin da tabi wajen dusashe karbuwar gwamnatin Trump dai akwai yadda a lokutan yakin neman zabe, ta rika caccakar tsohon shugaban kan yadda ya gaza dakile barnar da annobar Coronavirus ke yiwa Amurka ta fuskokin halaka rayuka da kuma durkusar da tattalin arziki.

Yanzu haka dai masu sharhi na cigaba da yin tsokaci kan tarihin da Kamala Harris ta kafa a Amurka, kuma Na’imatu Abdullahi Yamboni, wata ‘yar jarida daga birnin Kumasi na kasar Ghana na daga cikin wadanda suka yi sharhi kan mataimakiyar shugaban Amurkan ta farko a tarihi.

Na'imatu Abdullahi kan tarihin da Kamala Harris ta kafa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.