Amurka

Shugabannin duniya sun mika sakon fatan alheri ga Biden

Fadar gwamnatin Amurka ta White House
Fadar gwamnatin Amurka ta White House Reuters

Shugabannin kasashen Duniya da dama sun mika sakon fatan alheri ga sabon shugaban Amurka Joe Biden.

Talla

Tarayyar Turai ta bakin Ursula Von der Leyen sunyi maraba ta Biden tare da bayyana cewa a yanzu Turai na da babban aboki a fadar White House, bayan bakaken shekaru hudu na Trump, kuma wannan rana na cike da sabbin alherai.

Yayin da Charles Michel na Majalisar zartarwar Turai yace zuwan Biden zai kara karfin Tarayyar Turai, haka da Amurka, sannan a samu duniya mai tabbas, shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier, yace yanzu duniya baki daya ta sheda da sakewa tare da ficewa daga zama cikin rashin tababs, shi kuma Firaministan birtaniya Boris Johnson yace zasu kara hulda da Amurka a fannonin yakin da cutar corona, canjin yanayi, tsaro da bunkasa demokaradiya.

Sakataren kungiyar Nato a nasa waje Jens Stoltenberg yace duniya a yanzu babu wanda ya ishi kansa don haka dole a tafi tare, kakakin fadar Kremlin Dmitri Peskov cewa yayi ci gaba da kyaukyawar hulda tsakaninsu ya danganta ne da niyyar Amurka, shima tsohon shugaban Tarayyar Sobiyat na karshe Mikhaïl Gorbatchev, yayi fatan hulda mai kyau da Amurka da cewa rashin ta shine babban dar dar ga duniya.

Magabatan Iran sun ji dadin tafiyar Trump sosai wanda shugaban kasar Hasan Rohani a wani jawabi ta talbiji yayi fatan dawowar Amurka a yarjejeniyar Nukiliyar da suka cimma a 2015, yace Trump ba wai kasarsa ta Amurka ya jawowa matsaloli ba, ya zama babbar matsala da barazana ne ga duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.