Amurka

Tarihin sabon shugaban Amurka Joe Biden

Sabon shugaban Amurka Joe Biden
Sabon shugaban Amurka Joe Biden REUTERS/Brendan McDermid

Yau Laraba 20 ga watan Janairu Joe Biden na jam’iyyar Democrat zai yi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban Amurka na 46, wanda zai maye gurbin Donald Trump na jam’iyyar Republican, shugaba mai barin gado.

Talla

An haifi Joseph Biden a shekarar 1942 a Pensylvaniya, kuma ya fito daga gidan mabiya addinin Kirista na darikar Katolika da suka fito daga yankin Ireland.

Mahaifinsa bafaranshe ne da yayi gudun hijira zuwa Birtaniya.

Joe Biden yayi karatu a fannoni da dama, ciki har da Tarihi da Siyasa a jami’ar Delaware, sai kuma aikin Lauya a Jami’ar Syracuse, inda ya hadu da matarsa ta farko Neilia Hunter malamar makaranta, wadda ta rasu tare da ‘yarsu daya a cikin wani hadarin mota a shekarar 1972.

A shekarar 1977, Joe Biden ya sake aure da Jill Tracy Jacobs, itama malamar makaranta, wadda itama suka haifi ‘ya daya.

Bayan kasancewarsa dan majalisa a karamar hukumar New Castle na tsawon shekaru biyu an zabi Joe Biden a matsayin dan majalisar dattawa daga Delaware a jam’iyar Democrats a shekarar 1972, mukamin da ya rike har aka zabe shi matsayin mataimakin shugaban kasa a 2008 tare da shugaba Obama, har zuwa 2016.

Ranar 18 ga watan Agustan bara jam’iyarsa ta Democrats ta tsayar da shi a matsayin dan takarar shugaban kasa da mataimakiyarsa Kamala Harris, sun kuma lashe zaben shugabancin na Amurka da ya gudana a ranar 3 ga watan Nuwamba da gagarumin rinjaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.