Turai ta bukaci akai tare da sabon shugaban Amurka Biden.

Tutar Tarattar Turai
Tutar Tarattar Turai Kenzo TRIBOUILLARD / AFP

Kungiyar Turai ta sake bayyana fatan ganin sabon Shugaban Amurka Joe Biden ya mutunta wasu daga cikin yarjejeniyoyi da tsohon Shugaban kasar Donald Trump ya watsar, Kalaman shugabar hukumar zartarwa ta Turai Ursula Von Der Leyen a gaban wakilan kasashen na Turai dai-dai lokacin da ake ranar da  Joe Biden.

Talla

Kamun ludan Joe Biden zababen shugaban Amurka bayan shekaru hudu na mulkin Donald Trump ya faranta ran da dama daga cikin aminan Amurka.

A dai dai lokacain da Rasha ke bayyana fatan ganin sabuwar gwamnatin Amurka ta sake fasalta tsarin siyasar ta da sauren kasashen Duniya, kazalika Iran ta ce kalo ya koma bangaren Joe Biden a wannan sabuwar tafiya.

Sai dai jim kadan da bayyana matsayin su,kungiyar tarrayar Turai ta bakin shugaban hukumar gudanarwa ta Turai Usurla Von Der leyen a yayinda da take gabatar da jawabi a zauren majalisar Turai, ta ce wannan rana ta laraba na tamkar babbar rana domin Amurka daga rana mai kama ta yau za ta dawo jerryn kasashe dake tasawa da kungiyar Turai.

Shugaban Jamus Frank Walter Steinmeier ya bayyana farin cikin sa tareda kungiyar Turai da sunan daddadiyar abikiyar tafiyar Amurka a fanonin da suka shafi tattalin arziki,kimiya,kiwon lafiya,tsaro da sauren su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.