Wasanni

Burnley ta kawo karshen wasanni 68 da Liverpool da buga a Anfield ba'a doke ta ba

'Yan wasan Liverpool da Burnley
'Yan wasan Liverpool da Burnley Reuters

Burnley ta kawo karshen wasanni 68 da Liverpool da buga Anfield ba ayi nasara a kanta ba.

Talla

Wasanni 68 da Liverpool tayi na Premier ba a doke ta ba a Anfield ya zo karshe ne, bayan da Burnley ta doke ta da ci 1-0 a wasansu na daren Alhamis.

Wannan na nufin cewa, tawagan Jurgen Klopp sun gaza yin nasara a wasanni biyar da suka buga a jere, lamarin da ke neman ruguza damar kare kabbinsu, ganin cewa ratar maki shida ke tsakanin su da Manchester United dake jan ragamar teburin, a matsayi na hudu.

Rabon Liverpool ta dandana shan kashi a Anfield tun a watan Afrelun shekarar 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.