Wasanni

Kocin Marseille na cikin matsin lamba bayan shan kashi a hannun Lens

Yan wasan Olompigue du Marseille na Faransa
Yan wasan Olompigue du Marseille na Faransa NICOLAS TUCAT / AFP

Kocin Marseille na kasar Faransa Andre Villas-Boas na cikin matsi lamba tun bayan da kungiyar sa ta sha kashi hannun Lens da ci daya mai ban haushi.

Talla

Villas-Boas ya ce zai bar aikinsa a matsayin kocin Marseille idan shugabannin kungiyar suka bukaci hakan, bayan rashin nasarar da sukayi a gidan a gasar da Ligue 1.

Yanzu haka Olompic du Marseile ta kasance ta shida a kan teburin Lig 1, duk da cewa tana da wasa a hannu, da maki 10 tsakaninta da PSG da ke jan ragamar teburin, Lille ke matsayi na biyu.

Wasa daya kawai ta ci a wasanni takwas da ta buga a dukkannin gasannin wannan kaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.