Amurka

Majalisar dattawan Amurka ta tsaida ranar fayyace makomar Trump

Majalisar dokokin kasar Amurka
Majalisar dokokin kasar Amurka REUTERS/Zach Gibson

Majalisar Dattijan Amurka za ta fara zaman tabbatar da kudurin tsige tsohon shugaban kasar Donald Trump a Litinin mai zuwa dangane da rikicin da ya haddasa a zauren majalisar, wanda ya kai ga kisan mutane 5 ciki har da jami’in tsaro guda a ranar 6 ga watan Janairu.

Talla

Da ya ke jawabi gaban zaman majalisar, shugaban masu rinjaye Sanata Chuck Schumer yace ya tattauna da shugabar Majalisar wakilan kasar Nancy Pelosi da ta jagoranci tsige tsohon shugaban karo na biyu, wadda kuma ta tabbatar masa cewa takardun tsigewar za su isa gaban Majalisar Dattijan a ranar Litinin.

Sanata Schumer ya ce majalisar dattawan wadda yanzu ke da rinjayen ‘yan Democrat za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen tabbatar da bukatar.

Yanzu haka dai majalisar da Dattijai ke da wuka da nama a hannunta game da tabbatar da kudurin tsige Trump, wanda ya yi bankwana da mulki a Larabar da ta gabata, 20 ga watan Janairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.