Faransa-Amurka

Biden ya maido da Amurka cikin yarjejeniyar sauyin yanayi na Paris

Sabon shugaban Amurka Joe Biden
Sabon shugaban Amurka Joe Biden AP Photo/Andrew Harnik

Fadar gwamnatin Faransa ta ce shugaba Emmanuel Macron da sabon shugaban Amurka, Joe Biden sun amince a kan batun da ya shafi sauyin yanayi da kuma yadda za su yaki annobar Cornavirus, a tattaunawarsu ta farko, ta wayar tarho tun da aka rantsar da sabon shugaban Amurka.

Talla

A jiya Lahadi shugabannin biyu sun kuma bayyana aniyarsu ta yin aiki tare don wanzar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya da kewaye, musamman ma a kan batun nukiliyar Iran, a ganawar da suka yi na tsawon sa’o’i 4 cikin harshen Ingilishi.

Tun da farko a wannan mako, sai da shugaba Emmanuel Macron ya jinjina wa sabon shugaban Amurka Joe Biden dangane da shawararsa ta maido da kasar cikin yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris, bayan da tsohon shugaba Donald Trump ya fice daga cikinta, yana mai zargin an tsara ta ne da zummar nakasa tattalin arzikin Amurka.

Wata sanarwa daga fadar gwamnatin Amurka ta White House, wacce ta bayyana Faransa a mataysayin dadaddiyar kawa, ta jaddada abin da shugabannin biyu suka cimma, musamman ta bangaren bunkasa tattalin arzikin duniya da kuma yadda za a tinkari batun China, Gabas ta Tsakiya da yankin Sahel.

Ta ce shugba Biden ya jaddada kudirinsa na karfafa dangantaka da Turai, musamman ta hanyar kungiyar tsaro ta NATO, da kuma aiki kud da kud da kungiyar Tarayyar Turai.

Shugaba Macron ya taba yunkurin kulla dangantaka mai armashi da Trump, amma daga bisani suka shiga takun saka a game da batun Syria, harajin Amurka a kan Faransa, da kuma janyewa daga yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris da tsohon shugaban ya yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.