Tarayyar Turai ta ce dole ne kamfanin AstraZeneca ta wadata kasashenta da Rigakafi

Kamfanin AstraZeneca.
Kamfanin AstraZeneca. REUTERS

Kungiyar EU ta gargadi kamfanonin da suka samar da rigakafin cutar Korona da cewar, tilas su samar da isasshen adadin alluran kamar yadda suka yi alkawari, don kaucewa fuskantar cikas ga shirin yi wa miliyoyin jama’a rigakafin annobar a Turai.

Talla

Gargadin na EU ya zo ne bayan da a makon jiya kamfanin AstraZeneca ya shaidawa kungiyar cewa, ba zai iya samar da adadin alluran rigakafin cutar Korona da yayi alkawari ba, saboda wasu dalilai, irin uzurin da kamfanonin Pfizer da BioNTech suka gabatar.

Sai dai a martaninta, kungiyar kasashen Turan ta ce a yanzu ba ta da zabin da ya wuce haramta safarar alluran rigakafin da kamfanonin nahiyar suka samar zuwa wasu sassan duniya, matakin da shugabar sashin lafiyar kasashen na EU Stella Kyriakides ta ce ba na son kai bane, illa kare hakkin da suka cancanci samu.

Jami’ar ta kuma ce ya zama dole daga yanzu kamfanonin na AstraZeneca, Pfizer da kuma BioNTech su rika neman izini a kan lokaci, kafin safarar alluran rigakafin cutar Korona zuwa kasashe marasa karfi.

Wata matsalar da ta kunno kai kuma shi ne rahotannin wasu kafofin yada labarun Jamus da ke cewa allurar rigakafin da kamfanin AstraZeneca ya samar ba ta da tasiri a tsakanin mutane masu shekaru, bayanin da ma’aikatar lafiyar kasar ta karyata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.