Turai-Covid-19

BioNTech da Aztrazeneca za su karawa EU miliyoyin alluran rigakafin Covid-19

Tun farko BioNTech na shirin baiwa EU allurai miliyan 600 amma ya sanar da kara mata wasu miliyan 75 na daban.
Tun farko BioNTech na shirin baiwa EU allurai miliyan 600 amma ya sanar da kara mata wasu miliyan 75 na daban. REUTERS/Dado Ruvic/Illustration/File Photo

Hadakar kamfanin harhada magunguna na Pfizer da BioNTech ya sanar da shirin karawa Turai adadin allurai miliyan 75 na daban, don cike gibin da nahiyar ke fuskanta, matakin da ke zuwa kwana guda bayan Astrazeneca ya amince da kara kashi 30 kan yawan alluran da tun farko ya amince zai bai wa EU duk da takun sakar da suka fuskanta a baya-bayan nan.

Talla

Tun farko hadakar ta BioNTech da Pfizer ta kulla yarjejeniyar sayarwa Tarayyar Turai alluran rigakafin miliyan 600 ne a rukunin farko amma sanarwarta ta yau ta sanar da kara adadin miliyan 75 don cike gibin da Nahiyar ke fuskanta, alluran da kamfanin ke cewa za su kammala isa Turai cikin kwanaki 15 masu zuwa.

Sanarwar ta hadakar Pfizer da BioNTech na zuwa sa’o’I kalilan gabanin taron gaggawa da Angela Merkel ta kira tsakaninta da kamfanonin harhada magunguna don tattauna kalubalen da ake fuskanta dangane da alluran rigakafin dai dai lokacin da Coronavirus ke ci gaba da yaduwa a kasashen Turai.

A yammacin jiya Lahadi ne shugabar Majalisar Turai Ursula von der Leyen ta sanar da cewa kamfanin Astrazeneca ya amince da kara yawan alluran da zai samarwa nahiyar da karin kashi 30 yayinda rukunin farko na alluran zai fara isa nahiyar a mako na biyu na watan nan.

A bangaren guda BioNTech ya bai wa rassansa 13 da ke Turai umarnin fara samar da alluran rigakafin cikin watan nan, matakin da zai rage kamfar maganin da nahiyar ke fuskanta da kuma samun wadatuwarsa a Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI