Faransa

Faransa ta fara shari'ar wasu mutum 3 da ake zargi da yunkurin harin ta'addanci

Mutanen 3 da kotu ke tuhuma yayin zaman shari'ar watan Satumban 2018.
Mutanen 3 da kotu ke tuhuma yayin zaman shari'ar watan Satumban 2018. AFP

Faransa ta fara shari`ar wasu `yan kasar 2 da wani dan Morocco guda da ake zargi da yunkurin kaddamar da harin ta`addanci, kafin jami’an leken asirin kasar su bankado mugun aniyarta su ta kafar intanet.

Talla

Kotun da ke birnin Paris na tuhumar mutanen uku da laifin shiga kungiyar ta`addanci tare da shirin kai hare-hare kasar ta Faransa, kuma muddun ta same su da laifi, za su fuskanci daurin shekaru 30.

Tun a shekarar 2016, wannan batu ya samu asali, lokacin da hukumar leken asirin Faransa ta DGSI, ta bankado musayar sakon sirri tsakanin mutanen uku da kungiyar IS ta shafin sadarwar Telegram, da ke bayani kan hanyar samun makamai a cikin kasar don tayar da zaune tsaye.

Jami`an leken asarin na Faransa sun tuntubi lambar ta Telegram, inda suka samu tabbacin cewar, jagoran kungiyar IS da ke Syria da ya kira kansa Sayyaf ne ke amfani da layin, lamarin da ya kai su ga kamen mutanen uku, Faransawa biyu da wani dan kasar Morocco guda.

Binciken kwakwaf da jami`an sukayi kan wadannan mutane uku, da kuma sakwannin Telegram ya tabbatar da cewar, a watan Yunin shekarar 2016, Sayyaf ya aika wa daya daga cikin mutanen tsabar kudi sama da euro miliyan 13, wanda aka ajiye a wata makabarta a anguwar Montparnasse da ke birnin Paris.

Kudin da sukayi amfani da shi wajen sayan makai su boye a wani daji da ke arewacin Faransa kafin su shiga hannu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI