Wasanni

Babu kamar Messi cikin shekaru 10 - IFFHS

Lionel Messi na Barcelona yayin wasan daf da na kusa da na karshe a gasar Copa del Rey
Lionel Messi na Barcelona yayin wasan daf da na kusa da na karshe a gasar Copa del Rey REUTERS/Jon Nazca

Hukumar Kula da Tarihin Kwallon Kafa da kididdiga ta Duniya, ta zabi Lionel Messi a matsayin dan wasan da ya fi kowa iya taka leda a duniya cikin shekaru goma da suka gabata a ajin maza.

Talla

Hukamar da ake kira International Federation of Football History and Statistic a Turance, ta baza mambobinta daga wasu kasashe 150 a duniya don nemo fitaccen dan wasa a cikin shekaru goman da suka gabata, gami da dan wasa mafi inganci a kowace nahiya.

Dan wasan mai shekaru 33 ya yi ta haskawa cikin wadannan shekaru duk da wasu kalubale da ya fuskata a cewar hukumar, inda ya dauki kofunan La Liga shida, kofuna biyar na Copa del Rey, Kofin Zakarun Turai biyu, da kuma Ballon d’Ors 6.

Ko a wannan kakar, duk da matsaloli da Barcelona ke fama karkashin sabon kocin ta Ronald Koeman, dan kasar ta Argentina ya zura kwallaye 12 kuma ya taimaka anci biyu a wasanni 18 na La liga, yayin da yaci kwallaye uku kuma ya taimakwa aka ci biyu a karawa hudu na Gasar Zakarun Turai.

Sauran `yan wasan da suka nuna bajintar iya taka leda a cewar International Federation of Football History and Statistic dake da cibiya a kasar Jamus, sun hada da Chiristiano Roaldo, da Andres Iniesta, Neymar Junior, Sergio Ramos, Manuel Neuer, Robert Lewandowski, da Gianluigi Buffon, Zlatan Ibrahimo, sai kuma Luka Modric a matsayi na goma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI