Wasanni

Real Madrid ta dare na 2 a teburin Liliga ba tare da zaratan 'yan wasan ta ba

'Yan wasan Real Madris yayin wasan da suka kara da Getafe a gasar Laliga
'Yan wasan Real Madris yayin wasan da suka kara da Getafe a gasar Laliga REUTERS/Sergio Perez

Real Madrid dake rike da kambin gasar Laligar Spain ta doke Getafe da ci 2 da 0, kuma ta haye matsayi na biyu kan teburin gasar.

Talla

Madrid ta yi wannan nasara ba tare da 'yan taran kungiyar ba, saboda rauni da suke fama ko dakatarwa.

Karim Benzema ne ya zura kwallon farko da ka, a mintuna na 59 da soma wasa kafin mai tsaron baya Ferland Mendy ya kara ta biyu.

Yanzu haka Real na bin Atletico da tazarar maki biyar, to sai dai Atletico na da kwanten wasanni biyu.

Wasan da daren jiya, Madrid ta yi shine ba tare da zaratan 'yan wasanta ba, irin su Eden Hazard, Sergio Ramos, Federico Valverdi, Toni Kroos da Alvaro Odriozola, to amma kocin Real Zinedine Zidane ya gabatar da tsari na ba saban ba na 3-4-3, kuma yayi nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI