Faransawa sun yi zanga-zangar adawa da dokar kuntata wa Musulmai
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A Faransa wasu mutane sun gudanar da zanga-zanga a birnin Paris yau Lahadi, domin nuna adawa da sabon kudurin dokar da gwamnati ta yi don yaki da masu tsattauran ra’ayin addinin musulunci.
Masu zanga-zangar kimanin 200 da suka hada da kungiyoyin musulmai da na kare hakkin bi’adama sun zargi gwamnati da nunawa musulmai wariya.
Sabon kudirin da tuni aka kai gaban Majalisar dokokin kasar har aka fara muhara a kansa, na daga cikin matakan da shugaban kasar Emmanuel Macron ke baiwa fifiko wajen yakar masu tsattauran ra’ayin addini akasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu