Rasha

Rasha: Kotu ta tabbatar da hukuncin daurin shekaru 2 a kan Navalny

Alexeï Navalny, jagoran 'yan adawan Rasha
Alexeï Navalny, jagoran 'yan adawan Rasha Mladen ANTONOV / AFP

Kotu dake birnin Moscow ta tabbatar da hukuncin daurin shekaru 2 kan jagoran ‘yan adawar Rasha Alexie Navalny.

Talla

Hukuncin na zuwa ne sa’o’i bayan da wata kotun a yau din ta yanke hukuncin tilastawa jagoran ‘yan adawar biyan tarar dala dubu 13, bayan samunsa da laifin bata sunan gwamnatin Rasha.

A yammacin Asabar, wata kotu ta daure fitaccen abokin hamayyar shugaba Vladimir Putin, Alexy Navalny a kan laifin bata suna, daya daga cikin dimbim laifukan da ake zarginsa da aikatawa, kuma yake fuskantar tuhuma a kan su tun da ya dawo daga Jamus, bayan da ya yi jinyar harin guba da aka kai mai, harin da ya zargi gwamnatin Rasha da aikatawa.

A zaman saurron karar na farko da aka yi, alkali Dmitry Balashov ya kori daukaka karar da Navalny ya yi, wanda yake neman aa dakatar d hukuncin da aka yi mi a kan zargin ruf da ciki a kaan wasu kudade na al’umma, zargin d ya bayyana a matsayin bi – ta – da – kullin siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI