Birtaniya

Filin jiragen sama na Heathrow ya tafka hasara mafi muni cikin shekaru 75

Filin Jiragen sama na Heathrow dake birnin London
Filin Jiragen sama na Heathrow dake birnin London AP - Kirsty Wigglesworth

Hukumar gudnarwar filin jiragen sama na Heathrow dake birnin Londona, yace sanar da tafka hasarar euro bliyan 2 da miliyan 300 a shekarar bara ta 2020, a dalilin tasirin da annobar Korona ta yi kan sufuri a fadin duniya.

Talla

Hasarar dai ita ce mafi muni da filin jiragen yayi cikin shekaru 75.

Rahoton yace a shekarar ta bara kadai, an samu raguwar miliyoyin fasinjojin dake sauka da tashi da kashi 73 cikin 100 a filin jiragen na Heathrow, duk da kasancewarsa daya daga cikin filayen jiragen sama dake kan gaba wajen hada hadar sufuri a duniya.

A shekarar 2019, fasinjoji akalla miliyan 81 ne suka yi balaguro daga filin jiragen saman na Heathrow, sai dai a 2020 da ta gabata, adadin ya ragu matuka zuwa fasinjoji miliyan 22, kuma fiye da rabin fasinjojin sun yi balaguron nasu ne daga filin jiragen saman cikin watanni biyu na farkon shekarar ta bara.

Sai dai hukumar gudanarwar filin jiragen tace tana da isassun kudaden da za ta iya tafiyar da harkokinta har nan da shekarar 2023.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.