Turai-Coronavirus

Shugabannin Turai na tattaunawa kan shawo annobar Korona

Shugabannin kasashen Turai 27 na gudanar da taro ta kafar bidiyo don tattaunawa kan matsalar annobar coronavirus
Shugabannin kasashen Turai 27 na gudanar da taro ta kafar bidiyo don tattaunawa kan matsalar annobar coronavirus AFP - FRANCISCO SECO

Shugabannin Kasashen Turai na ganawa a wannan Alhamis cikin matsin lamba domin tattaunawa kan shirin rigakafin coronavirus a nahiyar, yayin da suke fama da rarrabuwar kawuna game da matakin rufe kan iyakokinsu.

Talla

Taron na kafar bidiyo tsakanin shugabannin kasashen Turai 27, na zuwa ne bayan shekara guda da bullar annobar coronavirus, yayin da akasarin kasashen nahiyar  ke fama da barkewar cutar a karo na biyu ko kuma na uku kuma babu wata alamar sassauci.

Kazalika kasashen na fuskantar gagarumar barazanar yaduwar sabbin nau’ukan cutar ta coronavirus da aka gano a Birtaniya da Afrika ta Kudu.

Hukumomin Brussels sun gargadi gwamnatocin kasashen Turai shida da suka hada da Jamus game da daukar matakin takaita zirga-zirga a kan iyakokinsu kai tsaye, yayin da kasashen da suka dogara da yawon bude ido  ke matsin lamba don ganin an dage haramcin tafiye-taiyen a lokacin hutun bazara.

Yanzu haka gwamnatocin kasashen Turai na sa ran samun alluran rigakafin cutar masu yawan gaske daga watan Afrilu bayan kamfanonin Pfizer da BioNTech da Moderna sun kara kaimi wajen samar da rigakafin.

Akwai yiwuwar Turai ta kuma amince da rigakafin Johnson and Johnson nan da tsakiyar watan Maris.

Tarayyar Turai ta sha caccaka kan yadda ta yi jinkirin fara kaddamar da shirin yi wa al’ummarta rigakafin annobar ta coronavirus.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.