Turai-Coronavirus

Shugabancin EU zai fadada aikin samar da rigakafin Coronavirus

Shugabar hukumar gudanarwar EU Charles Michel da shugabar kungiyar EU Ursula von der Leyen.
Shugabar hukumar gudanarwar EU Charles Michel da shugabar kungiyar EU Ursula von der Leyen. AP - Olivier Hoslet

Shugabannin kungiyar Tarayyar Turai na Shirin sake bunkasa tsarin samarwa kasashen Nahiyar wadatattun alluran rigakafin Coronavirus dai dai lokacin da barazanar yaduwar sabon nau’in cutar ke ci gaba da karfafa.

Talla

Shugabannin kasashen 27 da suka faro taronsu ta bidiyon Intanet daga jiya Alhamis sun cimma matsayar saukaka samar da alluran cikin hanzari bayanda wani rahoto na baya-bayan nan ke cewa, da yiwuwar sabuwar nau’in Corona ta fantsama fiye da hasashen masana.

Haka zalika taron ya tattauna yadda za a shawo kan matsalar haramcin bulaguro da kulle iyakoki da wasu kasashen kungiyar ciki har da Jamus da Austria da kuma Jamhuriyyar Chech suka dauka.

Zuwa yanzu mutum dubu dari 5 da 31 cutar ta Coronavirus ta halaka a kasashen nahiyar Turai yayinda kungiyar ta yi cinikin alluran rigakafin biliyan 2 fin ninki 4 na yawan al’ummar kasashen kungiyar mai yawan jama’a miliyan 450, ko da yak e zuwa yanzu nau’in allurai 3 kungiyar ta aminta da su da suka kunshi na hadakar Pfizer da BioNTech sai Moderna kana AstraZeneca duk da cewa akwai bayanan da ke nuna yiwuwar kungiyar ta amince da allurar Johnson and Johnson a wata mai kamawa.

Taron karkashin jagoranci Charles Michel a Brussels ya tabbatar da cewa sabbin matakan da kungiyar ta dauka zai bayar da damar dawowar harkokin hada-hada a kasashen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.