Amurka-Rasha

Amurka ta sanyawa Rasha sabbin takunkumai saboda yunkurin kisan Navalny

Vladimir Putin na Rasha da Joe Biden yayin wata ganawarsu a 2011.
Vladimir Putin na Rasha da Joe Biden yayin wata ganawarsu a 2011. ALEXEY DRUZHININ POOL/AFP/Archivos

Amurka ta sanya sabbin takunkumai kan manyan Jami’an Rasha 7 Saboda zarginsu da yunkurin kashe jagoran adawar kasar Alexei Navalny bayan shayar da shi guba a bara.

Talla

Wani matakin hadin gwiwa tsakanin Amurka da Turai ya sake sabunta takunkumai ga manyan jami’an tsaron kasar ta Rasha dangane da yunkurin kashe jagoran adawar baya ga ci gaba da tsare shi a gidan yari yanzu haka.

Acewar wani babban jami’in Amurkan rahoton bincike na musaman ya nuna jami’an tsaron Rasha ne suka yi yunkurin kashe Navalny a ranar 20 ga watan Agustan bara.

Jami’in ya bayyana cewa takunkuman na Amurka ya shafi manyan jami’an gwamnatin Rashan 7, yayinda ya ce za su fitar da karin bayani a nan gaba kadan.

Amurkan cikin sakon sabbin takunkuman ta gargadi Rasha game da hadarin da ke tattare da amfani da guba kan ‘yan adawa.

Sai dai a martanin da Rashan ta mayar cikin sanarwar da Kremlin ta fitar tun a jiya Talata ta ce ko kadan takunkuman na Amurka da Turai baya tasiri a kanta.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.