Faransa ta haramta kungiyar masu tsananin kyamar baki a kasar

Mambobin kungiyar masu tsatsauran ra'ayi da kyamar baki da gwamnati ta haram ta a Faransa
Mambobin kungiyar masu tsatsauran ra'ayi da kyamar baki da gwamnati ta haram ta a Faransa AFP - BERTRAND GUAY

Gwamnatin Faransa ta haramta kungiyar nan na masu tsattsauran ra'ayi da tayi kaurin suna wajen tsananin kyamar baki da adawarta zuwarsu kasar, tare da daukar doka a hannunta.

Talla

Ministan cikin gidan Faransa Gerald Darmanin ya wallafa matakin haramta kungiyar da ayyukanta a fadin kasar, ta shafinsa na Twitter, yana mai cewa wanzuwarta na haifar da nuna wariya, da kiyayya da kuma tayar da hankali" sakamakon yadda take samun karbuwa daga gungun fararen fata masu tsattsauran ra'ayi.

Sabuwar dokar da ta haramta kungiyar, tayi la’akari da rassa da take da ita a kasashen Turai da dama, kuma za’a dauke ta amatsayin mayaka.

Darmanin yace, kungiyar ta samu gudummawa daga maharin nan da yakai hari masallacin Chrischurch na kasar New Zealand a shekarar 2019, wato Brenton Tarrant, inda ya harbe mutane 51 har lahira.

To sai dai, Clement Martin, kakakin kungiyar dake kiran kanta “Generation Identity"a turance dake da cibiya  a kudu maso gabashin birnin Lyon, ya ce zasu kalubalanci haramcin a babbar kotun gudanarwa ta Faransa.

Kungiyar na daukar doka a hannunta wajen hana baki shiga Turai, na baya-bayan nan, shine wani gagarumin aiki da tayi a watan Janairu, inda mambobinta sama da 30 suka taru a tashar Col du Portillon da ke kan iyakar Faransa da Spain, tare da wulakanta bakin haure.

Abin da ya janyo haramta kungiyar

Tun a ranar 26 ga watan Janairun da ya gabata ministan cikin gidan na Faransa  ya fara daukar wannan mataki na rushe kungiyar a hukumance, bayan wani kazamin farmaki da ‘ya’yanta suka kai wa baki kan iyakar kasar, wanda tuni wasu masu rajin kare hakkin bil’adama suka shigar da kara, yayin da gwamnati ita ma ta bude bincike.

Shugabar Jam'iyyar Masu Tsattsauran Ra’ayi a Faransa, Marine Le Pen, ta soki matakin gwamnati na Shirin rusa kungiyar, tana mai cewa hana fadin albarkacin baki ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.