Faransa-Kamaru

Faransa ta musanta zargin mara baya ga gwamnatin Kamaru da Paul biya

Wata ganawar shugaba Emmanuel Macron na Faransa da takwaransa na Kamaru Paul Biya.
Wata ganawar shugaba Emmanuel Macron na Faransa da takwaransa na Kamaru Paul Biya. Laurent Cipriani / POOL / AFP

Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta yi watsi da zargin da wani dan majalisar dokoki ya yiwa kasar cewa ta na mara baya ga gwamnatin kama karyar kasar Kamaru baya, inda ma’aikatar ke cewa Faransar na matsayin jagora da a kowanne lokaci ta ke jan hankalin shugaban kasar ta Kamaru Paul Biya kan ya rika mutunta dokokin hakkin dan adam.

Talla

Tun farko dan majalisar dokokin jam’iyar La République en Marche, Sébastien Nadot ne yayin wani jawabinsa gaban majalisar ya zargi Faransar da goyon bayan gwamnatin Kamaru duk da kisan gillar da ta ke yiwa fararen hula.

Cikin jawabin dan majalisa Sebestien Nadot ya ce goyon bayan da gwamnatin kasar ke bai wa Paul Biya ya sabawa tsarin koyarwar tarihinta dama martabarta yayinda kuma ya sabawa abokanan huldarta musamman al’ummar Kamaru.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch (HRW) a ranar juma’ar da ta gabata ta zargi sojojin Kamaru da cin zarafin fararen hula a yankunan dake amfani da turancin inglishi mai  fama  da tashe tashen hankullan ‘yan aware.

Kungiyar ta HRW ta ce a shekarar 2020 an yiwa mata akalla 20 fyade baya ga kashe wani namiji guda da kuma kame wasu 35 a garin Ebam na yankin masu amfani da turancin ingilishi, harin da kungiyar ta ce ya faru ne kwanaki 15 bayan kisan gillar Ngarbuh da ya janyo hankalin kasashen Duniya.

A bangare guda, Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa kan kisan fararen hula 23 da suka hada da  yara 15 hade da mata masu ciki su 2.

Sai dai Sakataren kasa a ofishin ma’aikatar harkokin wajen Faransa Jean-Baptiste Lemoyne ya ce babu ta yadda za a yi a dorawa Faransa zargin mara baya ga Kamarun duk da kasancewarta mai taka-tsan-tsan wajen kare hakkin dan adam.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.