Faransa-Sahel

Ma'aikatar tsaron Faransa ta kare matakin kasar a yakin da ta ke a Sahel

Ministar tsaron Faransa Florence Parly.
Ministar tsaron Faransa Florence Parly. AP - Thibault Camus

Ministocin harkokin waje da na tsaron Faransa sun kare matsayin kasar na ci gaba da yaki da ‘yan ta’adda a yankin Sahel, a daidai lokacin da Majalisar dokoki ke mahawara kan makomar yakin da kasar ta kwashe shekaru 8 ta na yi.

Talla

Ministan tsaron Faransa Florence Parly ta bayyana yaki da yan ta’addan a matsayin abinda ba zai tabbata har abada ba, sai dai ta ce a halin yanzu ba za su iya barin yankin ba saboda kawayen su sun bukaci su ci gaba da taimaka musu akai, yayin da batun tsaron Faransa da nahiyar Turai ya dogara da zaman lafiyar yankin.

Shi kuwa ministan harkokin waje John Yves Le Drian ya ce Faransa na yakin ne domin murkushe ‚yan ta’addar da ke kokarin kafa Daula, wanda hana su hakan ya haifar da kashe kashen da su ke aikatawa wajen kai hari domin hana zaman lafiyar yankin.

Mataimakin shugaban Jam’iyyar shugaba Emmanuel Macron a zauren Majalisar, Thomas Gassiloud ya ce gudanar da mahawara kan yakin a Sahel ya zama wajibi ganin yadda aka kwashe shekaru 8 sojojin Faransa na sadaukar da rayukan su abinda ya ke bai wa jama’ar kasar alfahari, duk da asarar rayukan dakaru 50 a fagen fama da kuma kashe euro biliyan guda kowacce shekara.

Dan Majalisar ya ce idan rahotan da aka gabatar musu ya tabbata tun bayan taron Pau da ya kunshi shugabannin kasashen Sahel, toh akwai damuwa kan yanayin tsaron yankin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.