Faransa-Coronavirus

Paris: 'Yan sanda sun hana shan barasa cikin jama'a tsawon makwanni 3

Wata mata a wani gidan shan barasa dake birnin Paris a Faransa. 21/11/2019.
Wata mata a wani gidan shan barasa dake birnin Paris a Faransa. 21/11/2019. REUTERS/Benoit Tessier

Rundunar ‘yan sandan Faransa ta yi shelar haramta shan barasa a bainar jama’a a birnin Paris, dokar da tace ta soma aiki daga yau Asabar.

Talla

Matakin dai ya biyo bayan bijirewa dokokin hana taron jama’a don dakile yaduwar annobar Korona da ake gani a birnin na Paris a makwannin baya bayan nan.

Dokar za ta cigaba da wanzuwa tsawon makwanni 3, inda daga lokacin za a sake Nazari kan kara wa’adin ta ko kuma janye ta.

Matakin farko na hukumomin Faransa a watan Fabarairu wajen soma haramta shan barasar a bainar jama’a ya shafi fitattun wurare ne a birnin Paris, sai dai hakan bai hana taruwar jama’ar a wasu wuraren ba, abinda ke zama barazana ga kokarin kasar na dakile kaifin annobar Korona da ke cigaba da yiwa kasar barna bayan sake barkewarta a zango na biyu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.