Brazil-Coronavirus

Yawan mutanen da Korona za ta rika kashewa kullum a Brazil ka iya kaiwa dubu 3

Wasu marasa lafiya da annobar Korona ta kwantar a wani asibiti dake birnin Sau Paulo a Brazil.
Wasu marasa lafiya da annobar Korona ta kwantar a wani asibiti dake birnin Sau Paulo a Brazil. AP - Andre Penner

Kwamitin kwararrun dake yakar annobar Korona a Brazil ya gargadi gwamnatin kasar da cewa, yawan rayukan da cutar ke lakumewa ka iya kaiwa dubu 3 a kowace rana, muddin ba a dauki matakan dakile aukuwar hakan ba.

Talla

Kwararrun sun yi gargadin ne, yayin mika rahoton da suka tattara kan halin da ake ciki dangane da yakar annobar Korona a kasar, wadda shugaba Jair Bolsonaro ke cigaba da yin watsi da tasirinta.

Yanzu haka dai an shafe makwanni biyu cutar na halaka mutane fiye da dubu 1 da 250 kowace rana a Brazil.

Kididdigar hukumomin lafiya ta nuna cewar bayan Amurka, Brazil ce kasa ta biyu da annobar Korona ta fi yiwa ta’adi inda ta kashe mutane akalla dubu 262 da 770 daga cikin ‘yan kasar kusan miliyan 11 da suka kamu da cutar.

Alkaluman hukumomin lafiya na kasa da kasa sun ce a jiya Juma’a kadai, rayukan mutane dubu 10 da 685 Korona ta lakume a sassan duniya, yayin da mutane dubu 450 da 657 suka kamu da cutar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.