Faransa-Coronavirus

Mazauna arewacin Faransa sun koma karkashin dokar kulle saboda Korona

Wata kasuwa a yankin Dinkirk a arewacin kasar Faransa.
Wata kasuwa a yankin Dinkirk a arewacin kasar Faransa. AP - Michel Spingler

Dubban mutanen dake zaune a yankunan arewacin Faransa ne suka sake komawa karkashin dokar kullen hana fitar dare a karshen makon nan, wadda ta soma aiki daga ranar Asabar.

Talla

A birnin Paris kuwa a ranar ta Asabar dokar haramta shan barasa a bainar jama’a ta soma aiki, domin hana cinkoson mutane saboda dakile yaduwar annobar Korona.

Alkaluman ma’aikatar lafiyar Faransa na baya bayan nan sun nuna cewar a halin yanzu kasha 2 bisa 3 na yawan wadanda suka kamu da Korona a kasar, sun harbu ne da sabon nau’in cutar.

Wani Bafaranshe yayin karbar allurar rigakafin cutar Korona a birnin Paris.
Wani Bafaranshe yayin karbar allurar rigakafin cutar Korona a birnin Paris. AP - Christophe Ena

A halin yanzu mutane dubu 88 da 300 annobar Korona ta kashe a Faransa tun bayan bulla a watan Disambar 2019 daga China tare da bazuwa zuwa sassan duniya.

Tuni dai aikin yiwa ‘yan kasar allurar rigakafin Korona ya yi nisa a Faransa, inda mutane akalla miliyan 3 suka samu karbar allurar, tare da fatan adadin ya kai mutane miliyan 20 na da zuwa watan Mayun da ke tafe.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.