Turai-Coronavirus

Sabbin nau'ikan Korona na yaduwa cikin gaggawa a sassan Turai - WHO

Iyaye da dalibai a wata makaranta dake birnin Brussels na kasar Belgium.
Iyaye da dalibai a wata makaranta dake birnin Brussels na kasar Belgium. AP - Francisco Seco

Hukumar lafiya ta duniya ta ce sabbin nau’ikan cutar Korona na cigaba da yaduwa cikin sauri a sassan Turai, duk da matakan dakile annobar da hukumomin kasashen nahiyar ke yi.

Talla

Alkaluman baya bayan nan da hukumar ta WHO ta fitar, sun nuna cewar a tsawon makon da ya gabata kadai, karin mutane miliyan guda aka samu sun kamu da cutar Korona a nahiyar Turai, kwatankwacin karin kashi 9 cikin 100 kan adadin da aka saba gani.

Tuni dai masana suka danganta hauhawar adadin masu cutar ta Korona a Turai da bullar sabbin nau’ikan cutar musamman wanda ya soma bayyana a Birtaniya da kuma ke cigaba da yaduwa cikin sauri a tsakanin kasashen kungiyar EU 27, inda ya fi kamari a Jamus, Faransa, Italiya, Birtaniya, da kuma Spain.

Binciken kwararrun hukumar WHO ya nuna cewar sabon nau’in cutar Koronar na Birtaniya ya zarta wanda aka saba gani karfi da kuma saurin yaduwa da akalla kashi 50 cikin 100.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.