Birtaniya

Kiris ya rage na kashe kaina saboda wariyar launi - Meghan

Yarima Harry tare da matarsa Meghan Merkel.
Yarima Harry tare da matarsa Meghan Merkel. AP - Frank Augstein

Uwargidan Yarima Harry, jikan Sarauniya Elizabeth ta biyu, wato Meghan Markle, ta ce ta yi tunanin kashe kan ta bayan auransu, saboda yadda aka dinga nuna mata banbancin launin fata a gidan Sarautar.

Talla

Yayin da take tsokaci kan dalilin da ya sa suka fice daga gidan Sarautar Birtaniya, Meghan tace anki ba ta taimakon da take bukata lokacin da ta fada cikin halin kuncin rayuwa, yayin da aka yi ta mata karya lokacin da ake bayyana fargaba kan launin fatar ‘dan da za ta haifa.

Meghan,mai shekaru 39, ta ce mijinta Harry ne ya bayyana mata halin da ake ciki kan fargabar da was uke yi dangane da launin fatar dan ta Archie. Sai dai dukkanin ma’auratan sun ki bayyana sunayen ;yan gidan Sarautar da suka aikata hakan.

Yarima Harry da matarsa Meghan.
Yarima Harry da matarsa Meghan. AP - Mosa'ab Elshamy

Meghan wadda mahaifin ta Bature ne, mahaifiyarta kuma bakar fata, ta shaidawa Winfrey Oprah a hirar da suka yi cewar, wannan ya sa taga babu dalilin cigaba da rayuwar ta.

Uwargidan Yariman tace ta cika da fargaba lokacin da mijin ta ya shaida mata matsayin Gidan Sarautar kan launin ‘dan da zasu haifa, abinda ya sa suka yanke hukuncin komawa Amurka da zama.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.