Faransa-Coronavirus

Asibitocin Paris sun cika sun batse sakamakon ta'azzarar Korona

Doctor Henri Faure and medical colleagues treat a patient suffering from the coronavirus disease (COVID-19) in the Intensive Care Unit (ICU) at the Robert Ballanger hospital in Aulnay-sous-Bois near Paris during the outbreak of the coronavirus disease in France, October 26, 2020
Doctor Henri Faure and medical colleagues treat a patient suffering from the coronavirus disease (COVID-19) in the Intensive Care Unit (ICU) at the Robert Ballanger hospital in Aulnay-sous-Bois near Paris during the outbreak of the coronavirus disease in France, October 26, 2020 REUTERS - GONZALO FUENTES

Rahotanni daga kasar Faransa sun ce yanzu sashen gobe da nisa na asibitocin dake Yankin birnin Paris sun cika makil da wadanda suka kamu da cutar korona, inda likitoci suka fara sallamar mutanen dake fama da wasu cutttuka zuwa gida domin samun gadaje.

Talla

Karuwar yawan mutanen na zuwa ne a daidai lokacin da jami’an gwamnatin Faransa ke shirin gudanar da wani taron gaggawa gobe Laraba domin nazarin halin da ake ciki, da zummar kauce wa killace jama’a.

Yanzu haka dokar hana fita ta karfe 6 na yamma na aiki tare da hana mutane fita a karshen mako a yankin arewacin Calais.

Hukumomi sun ce yanzu haka mutane 1,018 ke kwance a gobe-da-nisa daga cikin gadaje 1,050 da ake da su domin masu fama da cutar, kuma wannan ne karo na faro da aka samu mutane sama da 1,000 dake kwance a asibitin sakamakon cutar korona tun daga ranar 18 ga watan Nuwambar bara.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.