Faransa-Coronavirus

Corona ta tilasta rage yawan marasa Lafiya a asibitin Ile de France

Asibitin kula da masu Coronavirus a yankin Ile de France.
Asibitin kula da masu Coronavirus a yankin Ile de France. © Christophe SIMON/AFP

Hukumomnin lafiya a Faransa, sun bayar da umarnin rage yawan marasa lafiya wadanda ba cutar corona ce ta sanya kwantar da su a asibiti ba da akalla kashi 40, ciki har da wadanda ke dakon tiyata a sashen kula da marasa lafiya masu bukatar kulawar gaggawa.

Talla

Yankin Ile de France mai yawan jama’a miliyan 12 yanzu haka na da masu coronavirus 973 da ke cikin mawuyacin hali duk da cewa guraben mutum dubu 1 da 40 kadai ya ke da shi a sashen kula da masu cutar.

Babban daraktan Lafiya na Faransar Aurelien Rousseau, ya shaidawa AFP cewa guraben da aka kebewa masu cutar ta corona da ke cikin mawuyacin hali ya yi matukar karanci ga yankin wanda zai tilasta rage masu fama da sauran cutuka zuwa wasu yankunan la’akari da tsanantar cutar a yanzu.

Mr Rousseau ya yi gargadin cewa matukar ba a rage yawan marasa lafiyan da kef ama da wasu cutukan ba, ko shakka babu zuwa karshen mako za a rasa wajen kwantar da masu cutar ta Corona a yankin na Ile de France.

Tun bayan bullar sabuwar nau’in Coronavirus ake ci gaba da samun hauhawar masu dauke da cutar a yankin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.