Birtaniya

Sarauniyar Ingila ta kadu da labarin nuna wa Yarima Harry banbancin jinsi

Sarauniya Elizabeth ta Ingila.
Sarauniya Elizabeth ta Ingila. POOL/AFP/File

Fadar Sarauniyar Ingila ta ce zargin nuna wariyar jinsin da Yarima Harry da uwargidansa Meghan Markel suka yi lokacin da suka yi hira da wata tashar talabijin, ya girgiza Sarauniya Elizabeth ta biyu.

Talla

Sanarwar da fadar ta gabatar ta ce ran daukacin iyalan gidan Sarautar ya baci kan irin halin da Yarima Harry da uwargidansa Meghan suka shiga, kuma duk batun da ya shafi maganar jinsi abin damuwa ne matuka.

Sanarwar ta ce yayin da ake samun sabanin ra’ayi kan batun, matsalar na da matukar girma, kuma iyalan gidan Sarautar zasu magance ta a asirce, yayin da Harry da Meghan da kuma ‘dan su Arche za su ci gaba da zama abin kauna a gidan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.