Turai-Coronavirus

EU za ta karbi karin alluran rigakafin corona na Pfizer miliyan 4

Shugabar kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen.
Shugabar kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen. JOHN THYS AFP/File

Kungiyar Tarayyar Turai za ta karbi karin alluran rigakafin Coronavirus, na hadakar kamfanin Pfizer da BioNTech miliyan hudu, nan da makwanni biyu masu zuwa a kokarin da ta ke yi na yaki da cutar a gungun kasashenta 27.

Talla

Shugabar kungiya EU Ursula von der Leyen ta ce nan da karshen watan Maris kungiyar za ta fara rarraba alluran ga yankunan da cutar ta tsananta.

Wata sanarwar EU a Brussels matakin cimma jituwa kan karbar karin alluran da kuma rarraba su cikin gaggawa ga kasashen ya biyo bayan tsanantar cutar a wasu kasashen da yak ai su ga sanya dokar hana shige da fice.

Leyen ta bayyana cewa yanzu haka shirin ya yi nisa kan yadda za a rarraba alluran musamman a kassahe 6 ciki har da Jamus da cutar ke ci gaba da kisa.

Shugabar ta EU ta bayyana cewa akwai bukatar shawartar kasashe kan su fifita yankunan kan iyaka wajen rabon alluran rigakafin ganin cewa a yankunan ne cutar ta fi tsananta fiye da ko’ina.

Sanarwar ta ruwaito Leyen na cewa babbar barazana ce kuma fargaba ganin yadda cutar ke ci gaba da bazuwa musamman a kasashen Jamus Austria Faransa da kuma Italiya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.