Faransa-Coronavirus

Masu zanga-zanga a Faransa na son gwamnati ta janye dokar takaita walwala

Wasu masu zanga-zanga a Faransa.
Wasu masu zanga-zanga a Faransa. REUTERS - BENOIT TESSIER

Dubban masu zanga-zanga a Faransa sun mamaye uku daga cikin manyan dakunan taruka guda 4 na kasar, inda su ke neman tilastawa gwamnati janye dokokin hana walwalar da ta kakaba musu da zummar dakile ci gaba da yaduwar annobar corona da ta sake barkewa a zango na biyu.

Talla

Tun cikin watan Oktoban bara ne gwamnatin Faransa ta rufe ilahirin dakunan taro, gidajen shallo da na bukukuwan nuna al’adu, kuma har yanzu ba a bude su ba, duk dacewar sassauta dokar kullen yaki da annobar Korona ta bada damar sake bude mafi hada-hadar kasuwanni.

Zanga-zangar Faransawan na zuwa bayan da a makon jiya wani rahoto ya nuna cewar annobar corona da ta tagayyara tattalin arzikin Duniya ba ta hana masu zuba hannun jari kauracewa kasar Faransa ba.

Rahoton da hukumar bunkasa ci gaban kasuwanci ta Faransa ta fitar, ya nuna cewar a shekarar 2020 kadai lokacin da cutar ta kai kololuwa, manyan ayyuka akalla dubu 1 da 215 masu zuba hannayen jari suka sanya kudadensu a ciki.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.