Sarauniyar Ingila ta bayyana damuwa biyo bayan wasu alamun nuna wariyar jinsin

La Reine Elisabeth II et le Prince Philip, duc d'Edimbourg lors d'un déplacement au sud de l'Angleterre le 4 juin 2016
La Reine Elisabeth II et le Prince Philip, duc d'Edimbourg lors d'un déplacement au sud de l'Angleterre le 4 juin 2016 GLYN KIRK / AFP

Fadar Sarauniyar Ingila tace zargin nuna wariyar jinsin da 'Yarima Harry da Uwargidan sa Meghan Markle suka yi lokacin da suka yi hira da talabijin, ya girgiza Sarauniya Elizabeth ta biyu.

Talla

Sanarwar da fadar ta gabatar tace ran daukacin iyalan gidan Sarautar ya baci kan irin halin da Yarima Harry da uwargidan sa Meghan suka shiga, kuma duk batun da ya shafi maganar jinsi abin damuwa ne matuka. 

Sanarwar tace yayin da ake samun sabanin ra’ayi kan batun, matsalar na da matukar girma, kuma iyalan gidan Sarautar zasu magance ta a asirce, yayin da Harry da Meghan da kuma ‘dan su Arche zasu cigaba da zama abin kauna a gidan.Sarauniyar Ingila da nuna bacin ran ta ,ya sa da dama daga cikin yan kasar soma bayyana ra'ayin su, ana sa ran nan gaba  za a dinga kaucewa fadawa irin wadanan matsalolli a fadar sarautar ingila.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.