Wasanni-Kwallon kafa-Spain-Italiya

Zidane ya ce dawowar Ronaldo Real Madrid abu ne mai yiwuwa

Cristiano Ronaldo na kungiyar Juventus.
Cristiano Ronaldo na kungiyar Juventus. AP - Luca Bruno

A ranar Litinin Zinedine Zidane ya bada haske a kan yiwuwar dawowar Cristiano Ronaldo  Real Madrid, inda ya ce lallai yana iya yiwuwa, bayan da wata kafar yada labaran Italiya ta tambaye shi ko ina gaskiyar cewa dan wasan gaban zai sake komawa Madrid.

Talla

Rahotanni daga Spain na nuni da cewa Ronaldo ya kagara ya koma Real Madrid , inda ya samu manyan manyan nasarori a shekaru 9 da ya yi wasa kafin barinsa zuwa Juventus a shekarar 2018 a kan kudi Yuro miliyan 100.

Kasancewar Ronaldo a kungiyar Juventus ba ta zamo mai da nasarori ba kamar yadda aka kyautata zato.

Kungiyar na a matsayi na 3 a teburin gasar Serie A, a yayin da doke su da Porto suka yi a wasan zakarun Turai   a makon da ya wuce ya sa yanzu karo na biyu kenan a jere suke ficewa a matakin kungiyoyi 16.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.