Birtaniya-Nukiliya

Birtaniya na shirin kara yawan makaman Nukiliyar da ta mallaka

Firaministan Birtaniya Boris Johnson.
Firaministan Birtaniya Boris Johnson. Leon Neal POOL/AFP/File

Birtaniya ta sanar da shirin kara yawan makamanta na Nukiliya a wani yunkuri na bai wa kanta kariya da kuma karfafa bangaren tsaronta, matakin da ke matsayin tufka da warwara ga shirinta a baya na kwance wasu makaman na Nukiliya bayan kawo karshen yakin cacar baka.

Talla

Karkashin shirye-shiryen da Birtaniyar ta kaddamar jiya Talata, da ke da nufin karfafa bangarorin tsaro da manufofinta na ketare ta ce za ta kara yawan kawunan makaman Nukiliuyar da ta ke da su daga kai fiye da 260 zuwa wani adadi mai yawa a nan gaba.

Yayinda a bangare guda kuma za ta fadada alakarta da kasashen nahiyar Asia baya ga duba kan alakarta da Rasha, batutuwan da ke matsayin mafi girman sauye-sauye da za ta samar wanda zai sauya fasalin yadda ta ke tafiyar da tsare-tsarenta a baya

Kunshin shirin mai shafuka 120 da Birtaniyar ta gabatar jiya Talata ya yi mi’ara koma baya kan matakin da ta ke ada na dakatarwa ko kuma kwance wasu makaman Nukiliyar da ta mallaka daga 260 zuwa 180.

Firaminista Boris Johnson da ke tsokaci kan shirin wanda aka yiwa lakabi da Birtaniya a cikin yanayin da Duniya ta shiga gasar kera makamai, ya ce Rasha ita ke matsayin babbar barazana ga tsaron kasar.

A cewar Johnson wajibi ne Birtaniya ta tashi tsaye wajen tara yawan makaman da za ta kare kanta da al’ummarta tsaronta da kasuwancinta da kuma uwa uba Demokradiyya.

Firaministan na Birtaniya ya bayyana cewa tun fil azal kasar na da shirin karfafa sashen tsaronta hanyar bunkasa makmaanta na Nukiliya tun bayan karewar yakin cacar baka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.