Faransa

Adadin sabbin kamuwa da Corona a Faransa ya zarta na watanni 4 a baya

Dakin kula da masu Coronavirus a Paris.
Dakin kula da masu Coronavirus a Paris. REUTERS - BENOIT TESSIER

Kasar Faransa ta sanar da samun yawan mutanen da suka kamu da cutar korona mafi yawa a ranar Laraba, wanda shi ne irin sa na farko a kusan watanni 4 da suka gabata, yayin da ake shirin killace birnin Paris domin takaita zirga zirga.

Talla

Ma’aikatar lafiyar kasar ta ce a ranar laraba, sabbin mutane dubu 38 da 501 aka tabbatar sun harbu da cutar, sabanin dubu 29 da 975 da aka gani a ranar Talata, kuma shi ne adadi mafi yawa tun watan Nuwambar bara.

A ranar Talatar da ta gabata, Firaministan kasar Kean Castex ya ce za su saka sabuwar dokar takaita zirga zirga a yankin Paris, irin wadanda aka saka a yankunan Nice da Calais wanda ake hana mutane barin gidajen su a karshen mako.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.