Faransa-Iran

Faransa ta roki Iran kan ta takaita shirin mallakar Nukiliyarta

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. Reuters

Shugaba Emmanuel Macron ya roki kasar Iran da ta daina zafafa batun aikin nukiliya da ta ke yi, wajen bijirewa sharuddan da manyan kasashen Duniya suka kulla da ita a shekarar 2015.

Talla

Shugaba Emmanuel Macron ya  fadawa manema labarai da ke rakiyar Shugaban Israela  Reuven  Rivlin yayin ziyararsa a Paris, cewa dole ne Iran ta daina dagula matakan da ake dauka don ceto yarjejeniyar ta hanyar kin mutunta tanade-tanaden da yarjejeniyar ta kunsa.

Macron ya bayyana cewa ala tilas wajibi ne kasar ta Iran ta nuna dattaku tare da kuma da yin taka-tsan-tsan wajen kiyaye yarjejeniyar.

Sabuwar Gwamnatin Amurka ta Shugaba Joe Biden ta nuna a shirye ta ke, ta sake komawa yarjejeniyar da aka kulla da Iran a 2015, wanda  tsohon shugaba Donald Trump ya sa kafa ya shure, amman kuma har ya zuwa wannan lokaci babu alamun Iran ta karbi goron tayin.

A cewar Emmanuel Macron Faransa a shirye ta ke don ganin an sake rungumar yarjejeniyar da aka kulla ta yadda za’a sa idanu kan ayyukan nukiliyar.

Gwamnatin Joe Biden na Amurka ta ce za’a koma yarjejeniyar, idan Iran ta kiyaye da shruddan da aka gindaya mata amman kuma Iran ta hau kujeran naki tare da bayyanawa Amurkan cewa dole sai ta janye mata takunkuman da Donald Trump ya mayar mata kafin ta koma mutunta yarjejeniyar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.