Finland

Finland ce kasar da aka fi jin dadi da farin ciki a duniya

Wani dan sanda bisa babur kusa da fadar gwamnatin Finland.
Wani dan sanda bisa babur kusa da fadar gwamnatin Finland. AFP

Wani rahoton masana dake samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da cewa duk da matsalolin annobar cutar coronavirus da ake fama dashi, kasar Finland ta kasance a kan gaba a duniya wajen kyautata rayuwar bil’adama, karo na hudu kenan a jere da kasar ke zama ta farko a duniya.

Talla

Rahoton da gogaggun masanan suka fitar a jiya Juma'a dake bayyana kasashen da aka fi jin dadi a duniya, wanda karo na 9 kenan a jere, ya tattaro bayanai daga kasashen duniya 149 inda aka yi binciken kwakwaf, ta fannoni da yawa, da suka hada da ‘yancin walwala, batun cin hanci da rashawa kafin masanan su cinki Finland a matsayin aljannar duniya.

Kasa ta biyu inji masanan ita ce  Denmark, sai kuma kasar Switzerland, sai Iceland da kuma Netherlands.

Kasar New Zealand wadda ta zo ta 9, ta kasance wadda bata cikin kasashen Turai da ke rukunin kasashe da ke sahun gaba .

Jamus ta kasance  13 yayin da Faransa ke matsayin ta 21.

A nahiyar Africa kuma kasashen da suka taka rawar gani sun hada da  Lesotho, sai Botswana, sai Rwanda sai Zimbabwe dake chan kasan tebur, amman duk da haka     tafi kasar Afghanistan.

Kasar Finland dai ta kasance tana da yawan mutane  kasa da miliyan 6, ga kowa cikin wadata, ga kyakkyawan tsaro da zaman lafiya, ga yalwan arziki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.