Dokar hana zirga-zirga ta haifar da zanga-zanga a yankin Turai
Wallafawa ranar:
Dubban jama’a ne suka gudanar da zanga-zanga a sassan nahiyar Tuari don nuna adawar su dangane da sabon matakin da hukumomin kasashen suka dau na sake takaita zirga-zirga dama kulle wasu sassan daban.
Jamus,Netherland,Austria,Bulgaria,Suiziland,Sabiya, Fologne,Faransa da Birtaniya,hade da Canada na daga cikin yankunan da jama’a suka fito don nuna bacin ran su dangane da wadanan matakai don yakar yaduwar cutar Coronavirus.
Ana dai bayyana cewa akalla mutane 36 ne yan sanda a Birtaniya ke tsare da su yanzu haka,inda ake bayyana cewa yan Sanda da dama ne suka samu rauni a birnin Landan,yayinda a Faransa kusan mutane milyan 21 za su kasance a gidajen su kamar dai yada hukumomin kasar suka sanar.
A Fologne yanzu haka hukumomin sun umurci yan kasar da su kasance a gidajen su tsawon makonni uku,tareda kawo sassauci a matakin kule su,inda wasu daga cikin wurarren shakatawa kama daga Otel,Cinema,gidan kalo za su kasance a bude.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu