Italiya-Mafia

Fafaroma ya bayyana Mafiya a matsayin 'kungiyar masu aikata zunubi'

Fafaroma Francis, shugaban darikar Katolika
Fafaroma Francis, shugaban darikar Katolika AP - Hadi Mizban

Shugaban Mabiya darikar Katolika na duniya Fafaroma Francis ya yi mummunar suka kan kungiyar masu aikata laifuffukan da ake kira mafiya a ranar da ake bikin tuna irin mutanen da kungiyar ta yi wa illa a kasar Italiya.

Talla

Fafaroman ya bayyana cewar ana da irin wadannan kungiyoyin ta mafiya a kowanne sashe na duniya, kuma suna amfani da annobar korona da ta addabi duniya wajen azurta kan su ta hanyar cin hanci da rashawa.

Shugaban mabiya darikar Katilikan ya ce Fafaroma St John Paul na biyu ya soki yadda mafiyar ke kashe mutane, yayin da Fafaroma Benedict na 16 ya bayyana su a matsayin hanyar mutuwa.

Fafaroma Francis ya bayyana kungiyar mafiyar a matsayin kungiyar masu aikata zunubi, wadanda ke musayar imanin su da gumaka sabanin abin da addinin Kirista ya tsaya a kai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.