Faransa za ta sauya fasalin yiwa jama'arta allurar rigakafin coronavirus
Wallafawa ranar:
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya ce gwamnatin kasar za ta fara yi wa jama’ar ta allurar rigakafin Corona, ba kakkautawa a dai-dai lokacin da cutar ke kara bazuwa a sassan kasar, ta yadda za a sauya jadawalin rigakafin ba dare-ba-rana don dakile yaduwarta.
Shugaba Macron ya ce abin fargaba ne yadda cutar corona ke kara mamayar jama’a, wanda yanzu asibitoci a birnin Paris sun cika makil da marasa lafiya a cewar shugaban.
Macron ya ce za a fara wannan aikin rigakafin na ba dare ba rana a ranar 1 ga watan Afrilu, kuma babu wasu ranaku da za a tsallake a aikin.
Kasar Faransa dai a yanzu na kokawa ne da cutar da ta sake barkewa a karo na uku, kuma tana cikin kasashen da ke fama da karuwar sabbin masu kamuwa da cutar a kullu yaumun.
Ya zuwa yanzu dai kasar na da alluran rigakafin cutar sama da miliyan 11 sai dai duk da hakan cutar na ci gaba da yaduwa kamar wutar daji a sassan kasar.
Ministan Lafiya na Faransar Olivier Veran ya ce rundunar sojin kasar za ta samar da manyan cibiyoyin bayar da alluran rigakafin guda 35 a fadin kasar, don saukaka aikin da kuma gaggauta yiwa jama'a.
Kawo yanzu dai kasar ta Faransa ta dogara ne da asibitocin cikin unguwanni da dakunan shan magani da na tiyata a matsayin wajen killace masu fama da cutar, a yayin da sauran kasashen turai ke amfani da filayyen wasanni.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu