Faransa

Turkiya na yunkurin yi mana katsalandan a zabe- Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron AP - Gonzalo Fuentes

Turkiya ta danganta kalaman shugaban Faransa Emanuel Macron da suka zargeta da yunkurin  yin katsalandan a cikin harakokin zaben Faransa mai zuwa da cewa ba abin amincewa ba ne.

Talla

A lokacin da yake shaguben nuna yatsa ga kasar ta Turkiya  a wani shiri  da talabijin din Farance 5 ta yada,   shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce  babu shakka ana fuskantar barazanar katsalandan a cikin harakokin zaben na Faransa mai zuwa.

Emmanuel Macron Shugaban kasar faransa
Emmanuel Macron Shugaban kasar faransa REUTERS - POOL

Sai dai wata sanarwa da ma’aukatar harakokin wajen Turkiya ta bayyana furcin na Macron da zama kuskure, kuma hali ne da zai iya haifar da cikas ga kawance da amintakar dake tsakanin kasashen 2

sanarwar ta kara da cewa Turkiya na da abubuwa dake gabanta, a game da abinda ya shafi Siyasar cikin gidan Faransa ba abinda Turkiya ke fata illa ganin al’ummarta dubu dari 800 dake zaune a Faransa sun ci gaba da kasancewa cikin farin ciki da kwanciyar hankali

Zargin na  M. Macron dai na zuwa ne a dai dai lokacin da turkiya ke kokarin ganin an samar da sassauci ga huldar diplomasiyar da ta yi tsauri tsakaninta da kasashen turai da dama da suka hada da Faransa.

Alaka tsakanin mahukumtan Paris da Ankara mambobi 2 a kungiyar tsaro ta Nato, ta yi tsauri ne sanadiyar batutuwa da dama da suka hada da rikicin kasshen Syriya  Libiya da kuma rikicin yammacin tekun Méditerranée. 

Abinda ya haifar da masayar kalamai masu zafi tsakanin Recep Tayyip Erdogan da  Emanuel  Macron.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.