Faransa-Rwanda

Bincike ya wanke Faransa daga zargin hannu a kisan kiyashin Rwanda

Shugaba Emmanuel Macron rike da rahoton binciken da ke wanke kasar da zargin hannu a kisan kiyashin Rwanda na 1994 tare da masanin tarihin kasar Vincent Duclert a fadar Elysee yau juma'a.
Shugaba Emmanuel Macron rike da rahoton binciken da ke wanke kasar da zargin hannu a kisan kiyashin Rwanda na 1994 tare da masanin tarihin kasar Vincent Duclert a fadar Elysee yau juma'a. © AFP - Ludovic Marin

Kwamitin binciken da shugaba Emmanuel Macron ya kafa kan kisan kiyashin da aka yi a kasar Rwanda na shekarar 1994 ya zargi Faransa da daukar nauyin wani kaso na abinda ya faru wajen kauda kan ta daga shirin kisan, yayin da ya ce babu hannun kasar wajen kashe-kashen da aka yi.

Talla

Rahotan binciken da aka gabatarwa shugaba Emmanuel Macron ya bayyana cewar akwai gazawa daga bangaren Faransa dangane da kisan kare danganin da ya lakume rayukan mutane 800,000 akasarin su yan kabilar Tutsi tsiraru wadanda aka yanka tsakanin watan Afrilu zuwa Yuli na shekarar 1994.

Binciken da masanan suka yi ya tabbatar da wani kaso na laifi dangane da manufar da shugaban kasa Faransa na wancan lokaci Francois Mitterand ya dauka.

Sanarwar da fadar shugaban kasa ta gabatar yace shugaba Macron ya yaba da rahotan wanda ke nuna gagarumar cigaba wajen fahimtar rawar da Faransa ta taka lokacin rikicin na Rwanda.

Sanarwar tace Faransa za ta cigaba da kokarin ganin an kawo karshen kama karya dangane wadanda aka samu da hannu alan laifuffukan yaki.

Da yawa daga cikin wadanda ake zargi da hannu a kisan kare dangin cikin su harda jami’an gwamnatin Rwanda sun gudu zuwa Faransa, yayin da kadan daga cikin su ne suka fuskanci shari’a.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.