Birtaniya

Birtaniya ta mayar da martani ga China kan sanyawa jami'anta takunkumi

Firaministan Birtaniya Boris Johnson.
Firaministan Birtaniya Boris Johnson. AP - Dominic Lipinski

Gwamnatin Birtaniya ta bayyana goyon baya ga daukacin mininistoci da manyan jami’anta wadanda China ta sanyawa takunkumi dangane da rawar da suke takawa wajen kalubalantar muzgunawa da cin zarafin da tsirarun musulmi ‘yan kabilar Uyghur ke fuskanta a kasar.

Talla

A wani sakon twitter da Firaminista Boris Johnson ya wallafa bayan matakin Chinar na sanya takunkumin kan ‘yan majalisar da wasu daidaikun al’ummar kasar, ya ce ko shakka babu ‘yan Birtaniya sun nunawa Duniya cewa babu gurbin keta hakkin dan adam bayan jajircewarsu kan ‘yan kabilar ta Uyghur.

Acewar Johnson dokokin Duniya sun bayar da ‘yancin tofa albarkacin baki kuma dakilesu babban kuskure ne da wasu ke yi yanzu haka, kalaman da kai tsaye ke shagube ga Chinar wadda ke yaki da dokar ta ‘yancin tofa albarkacin baki.

Chinar dai ta sanya takunkumi kan daidaikun al’ummar birtaniya 9 baya ga ‘yan majalisu da kososhin gwamnati 4 wadanda ta ce suna yada farfagandar karya kan yadda kasar ke azabtar da ‘yan kabilar ta Uyghur musulmi.

Ministan harkokin wajen Birtaniyar Dominic Raab ya ce suna gab da sammacin jakadan Beijing a London don yi musu bayani, yayinda ya kalubalancin china kan ta baiwa jami’an Majalisar Dinkin Duniya izinin shiga yankin Xinjing da ake ci gaba da tsare da ‘yan kabilar ta Uyghur matukar ta na bukatar wanke kanta daga zargin take hakkin bil’adaman da ake kanta.

Akwai dai bayanan da ke nuna yadda ‘yan kabilar ta Uyghur ke ci gaba da rayuwa cikin kaskanci baya ga azabtarwa da kuma kisan gilla baya ga tiilasta musu aikatau cikin kangin bauta ciki har da noman auduga da kuma haramtawa matansu haihuwa don kawar da kabilar daga ban kasa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.