Faransa-Magani

Kotu ta samu wani kamfanin magunguna a Faransa da kisan jama'a

Nau'in maganin na kamfanin Servier da ake zargin ya kashe tarin jama'a.
Nau'in maganin na kamfanin Servier da ake zargin ya kashe tarin jama'a. FRED TANNEAU AFP/File

Wata kotu a Faransa ta samu katafaren kamfanin sarrafa maganin rage kiba na Servier da ke kasar da laifin kisan daruruwan mutanen da suka yi amfani da maganin na cutar suga da kuma kwayar da ke rage kiba.

Talla

Kamfanin na Servier da ya shafe shekaru 33 yana samar da nau’in magungunan gabanin dakatar da shi a 2009 biyo bayan zargin nau’in maganin nasa na illa ga zuciya, anyi kiyasin cewar mutane sama da miliyan 5 su ka sha maganin kafin dakatar da amfani da shi, a kasar wadda ta yi shura wajen samun tangarda a bangaren masana’antunta na magunguna.

Tuni dai kotun ta aike da shugaban kamfanin gidan yari na shekaru 4 baya ga cin tararsa yuro miliyan 2 da dubu 700 saboda samun sa da laifin yaudara da kisan kai ba tare da niyya ba, yayin da kuma zai biya mutane sama da 6,500 diyya.

Mai shari’a Sylvie Daunis ta kuma ci tarar hukumar kula da kamfanonin harhada magunguna na kasar tarar yuro miliyan 303 kan samunsa da laifin sakaci ta yadda har maganin yayiwa dubunnan jama’a illa.

Mai shari’ar ta ce kamfanin ya sanya mutane nuna shakku kan harkokin kula da lafiya, yayinda suka ki daukar mataki bayan sun san illar da ya ke yi wa jama‘a.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.