Faransa-Makarantu

Macron ya bayyana shirin kulle ilahirin makarantun kasar saboda Corona

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. © RFI/Captura de vídeo

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana shirin rufe makarantun kasar daga makon gobe da kuma takaita zirga zirgar jama’a a fadin kasar domin dakile yaduwar cutar korona.

Talla

Macron yace daukar matakin ya zama wajibi sakamakon samun karuwar masu harbuwa da cutar da kuma raguwar matakan da ake dauka, yayin da yace samun nau’in cutar irin ta Birtaniya na nuna cewar suna fuskantar gazawa wajen matakan da suke dauka.

Saboda haka shugaban yace daga ranar litinin mai zuwa za’a rufe makarantu na makwanni 3, amma matakin ya kunshi hutun da ake na makwanni biyu.

Shugaban yace daga daren asabar zuwa makwanni 4 za’a sanya dokar takaita zirga zirga a fadin kasar baki daya da kuma rufe shagunan da bude su bai zama wajibi ba kamar yadda ake amfani da dokar a wasu sassa.

Sai dai Macron yace za’a bude wuraren al’adu da wasu shaguna a tsakiyar watan Mayu a karkashin dokoki masu tsauri wanda za’a bayyana nan gaba.

Shugaban ya kuma bayyana shirin gabatar da maganin rigakafi ga duk masu bukata daga cikin wadanda suka haura shekaru 60 daga ranar 16 ga watan Afrilu sai kuma masu sama da shekaru 50 daga ranar 15 ga watan Mayu.

Macron ya amsa cewar sun yi wasu kura kurai a baya, amma sun jajirce wajen daukar matakan da zasu kare lafiyar jama’ar kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.