Faransa-Kida

Corona ta tilasta dakatar da manyan bajekolin Turai shekaru 2 a jere

Bajekolin kide-kide na Eurocks da ke gudana shekara-shekara a Faransa.
Bajekolin kide-kide na Eurocks da ke gudana shekara-shekara a Faransa. SEBASTIEN BOZON AFP/File

Bukukuwan bazara a Turai sun zo a wani yanayi da ba a saba gani ba shekara ta biyu a jere bayan tsanantar Covid-19 duk da matakin yiwa miliyoyin jama’a rigakafin cutar a Nahiyar, wanda ya kai ga sake soke bukukuwan a wannan karon kamar bara, don dakile yaduwar cutar.

Talla

Sanarwar soke bukin bajekolin littattafan na Duniya da ke gudana a garin Angouleme na Faransa, shi ne matakin baya-bayan nan da mahukuntan Turai suka dauka, karkashin dokokin hana yaduwar cutar ta Covid-19.

A juma’ar nan ne mashirya bajekolin a Faransa suka sanar da dakatar da shi, bikin da bisa al’ada ke shirin gudana a karshen watan Yuni.

Matakin dakatar da bajekolin na watan Yuni ya biyo bayan, bukukuwan bajekolin kade-kade mafiya girma a nahiyar ta Turai da suka fuskanci makamanciyar dakatarwar shekara ta biyu a jere, wadanda suka kunshi bajekolin kide-kide na Solidays da Hellfest baya ga na Garorock da kuma Eurocks kari kan Lollapalooza da ke gudana a birnin Paris.

Gabanin sanarwar dakatar da bukuwan bajekolin na kide-kide akalla tikitai fiye da miliyan 1 aka sayarwa ‘yan kallo.

Baya ga bukukuwan na Faransa, mabanbantan bajekoli bakwai aka dakatar a Jamus da suka kunshi Deichbrand da bikin Hurricane da kuma Southside kana Rock am Ring da kuma Rock im Park baya ga SonneMondSterne da kuma Greenfield. 

Haka zalika bukuwan Sonar da Primavera a Barcelona ta Spain dukkaninsu sun sake fuskantar dakatarwa shekara ta biyu a jere.

Zuwa yanzu adadin alluran da EU ta iya samu kadai wanda zai ishi kashi 10 cikin 100 na al’ummarta ne wanda ke nuna dole kasashen suci gaba da daukar matakan takaita walwalar jama’a don dakile yaduwar cutar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.