Faransa-Adidas

Barayi sun lakadawa tsohon mai kamfanin Adidas duka a Faransa

Bernard Tapie fitaccen attajiri a Faransa kuma tsohon mamallakin kamfanin Adidas.
Bernard Tapie fitaccen attajiri a Faransa kuma tsohon mamallakin kamfanin Adidas. Bertrand GUAY AFP/Archivos

Rahotanni daga Faransa sun ce wasu barayi sun kutsa kai gidan tsohon minista kuma attajiri a kasar Bernard Tapie wanda ya taba mallakar kamfanin sarrafa kayayyakin wasanni na Adidas inda suka daure shi da matar sa, suka kuma lakada musu duka cikin dare.

Talla

'Yan Sanda sun ce barayin guda 4 sun shiga gidan su ne bayan 12 dare, inda suka lakada musu duka kafin daure su da wayar wuta, kafin su kwashe dukiyar da ke ciki.

Rahotanni sun ce uwargidan attajirin ta yi nasarar kubuta inda ta ruga gidan makota tare kuma da kiran jami’an 'yan sanda.

Magajin Garin yankin ya ce Tapie da uwargidan sa sun samu raunuka daga dukar barayin saboda rashin samun dukiyar da suke fata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.