Faransa-Tattalin arziki

Faransa za ta fuskanci gagarumin gibin tattalin arziki fiye da hasashe a bana

Ministan kudin Faransa Bruno Le Maire yayin jawabi kan halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.
Ministan kudin Faransa Bruno Le Maire yayin jawabi kan halin da tattalin arzikin kasar ke ciki. AFP - THOMAS COEX

Ministan kudin Faransa Bruno Le Maire ya ce gibin da ake samu a tattalin arzikin kasar zai kara fadi, zalika bashin da ke kan gwamnati zai karu, saboda tasirin annobar corona da ke barazanar mayar da hannun agogo baya.

Talla

Le Maire ya ce yanzu haka akwai fargabar gibin da su ke samu duk shekara ka iya kai wa kashi 9 cikin 100 akan ma’aunin tattalin arzikin kasar a wannan shekarar duk da irin makudan kudaden da shugaba Emmanuel Macron ke kashewa domin rage radadin tasirin annobar ta  coronavirus.

Alkalumman baya bayan nan da Ministan kudin Faransar ya bayyana sun yi hasashen bashin da ke kan gwamnatin kasar zai karu zuwa kashi 118 cikin 100, sabanin kasha 115 da aka yi hasashe.

Yanzu haka dai Faransa na fuskantar sake barkewar annobar corona a zango na uku, inda adadin masu kamuwa da cutar ya kai dubu 40 duk rana a makwannin baya bayan nan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.